Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Gwamnatin Shugaba Buhari Ta Bayyana Matsayin Da Ta Kai A 2021

Ministan yaɗa labarai Lai Mohammed ya ce gwamnatin shugaba Buhari ta samu nasara a fannoni da dama duk da an fuskanci ƙalubale na tsaro da ta tattalin arziki a shekara ta 2021.

Lai Muhammad ya bayyana haka ne a wajen wani taron manema labarai day a kira a nan Abuja.

Ya ce a shekara mai ƙarewa, babban ƙalubale shi ne na tsaro, amma duk da wannan da kuma ƙalubalen tattalin arziki da aka saba samu, wannan gwamnatin ta shugaba Buhari ta samu ci gaba sosai kamar yadda za a bayyanawa.

Ministan ya bayyana nasarorin da gwamnatin shugaba Buharin ta samu kamar bangaren tsaro, ya ce ya kasance wanda aka fi fuskantar ƙalubale cikin wannan gwamnati.

Lai Muhammad ya ce duk da ƙalubalen, dakarun rundunar Hadin Kai da ke aiki a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya sun kashe mayaƙa 1,000 da kuma 22,000 da suka mika kan su tare da ajiye makaman su da kuma iyalan su.

Exit mobile version