Home Labaru Gwamnatin Najeriya Za Ta Kashe Naira Biliyan 250 Don Rage Talauci Bana

Gwamnatin Najeriya Za Ta Kashe Naira Biliyan 250 Don Rage Talauci Bana

90
0

Gwamnatin tarayya ta amince a kashe naira biliyan 250 a
wannan shekarar, a shirin ta na rage talauci da ta ke
gudanarwa a faɗin Nijeriya.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana haka, yayin wani jawabi da ya yi a kan rahoton ci-gaban da aka samu a shirin rage talaucin na ƙasa a gaban kwamitin da ya jagoranta.

Ya ce ayyukan da aka tsara aiwatarwa a shekara ta 2023 a ƙarƙashin shirin dai, sun haɗa da gina gidaje dubu ɗari ga masu ƙaramin ƙarfi, aikin da zai samar da ayyukan yi miliyan ɗaya na kai-tsaye ko a kaikaice.

Akwai kuma faɗaɗa samun makamashi ta hanyar samar da fitilun gefen titi dubu 1 da 200 a yankunan karkara, da wasu ƙananan tashoshin lantarki da za a riƙa amfani da su a gonaki ƙarƙashin wani shiri mai suna Solar Naija.

Sai kuma samar da tallafin naira biliyan tara ga manoma masu ƙaramin ƙarfi a karkashin shirin samar da aikin yi a bangaren noma, da fadada rijistar mutanen da ke samun tallafin rayuwa da ƙarin magidanta miliyan uku.

Leave a Reply