Gwamnatin jihar Kwara, ta amince da ɗaukar matakin wucin-
gadi na rage adadin kwankin aikin gwamnati domin taimaka
wa ma’aikata wajen rage raɗaɗin da janye tallafin man fetur
zai haifar.
Shugabar ma’aikata ta jihar Mrs Susan Modupe Oluwole ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na gwamnan jihar Murtala Atoyebi ya fitar.
Mrs Oluwole, ta ce gwamnan jihar Abdulrahman Abdulrazaq ne ya bada umarnin rage kwanakin aikin gwamnatin na wucin-gadi daga kwanaki biyar zuwa uku a kowane mako.
Haka kuma, Mrs Oluwole ta umarci shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnati a faɗin jihar su gaggauta tsara wa ma’aikatan hukumomin su kwanakin da ya kamata su je aiki.

