Home Labaru Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Mika Mulki Ga Gwamnati Mai Jiran Gado

Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Mika Mulki Ga Gwamnati Mai Jiran Gado

96
0

Majalisar zartarwa ta Jihar Kano, ta amince da kafa kwamitin
mika mulki na mutane 17 ga gwamnati mai jiran gado a jihar.

Haka kuma, Majalisar ta amince da wani karamin kwamitin
mutane 100, wanda za a fitar da kundin tsarin mulki daga
ma’aikatu da hukumomi daban-daban a jihar Kano.

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar
Kano Malam Muhammad Garba ya sanar da haka a cikin wata
sanarwa da ya fitar.

Ya ce kwamitin zai kasance a karkashin jagorancin sakataren
gwamnatin jihar Kano Alhaji Usman Alhaji, wanda ya kunshi
shugaban ma’aikatan gwamnati da babban lauya kuma
kwamishanan shari’a da kwamishinan yada labarai da na
muhalli da kwamishinan kasuwanci.

Malam Garba ya kara da cewa, babban kwamatin zai yi aiki
cikin jituwa da nufin mika mulki a cikin makonni uku.

Leave a Reply