Gwamnatin jihar Kaduna ta tsawaita dokar hana zirga-zirga na tsawon makonnin biyu domin dakile yaduwar cutar Coronavirus a fadin jihar.
Gwamnan jihar Nasiru El-Rufai ya sanar da haka ta bakin mataimakiyar sa Hadiza Balarabe, tare da cewa an tsawaita dokar ne biyo bayan shawarwarin kwararru a kan harkokin lafiya, a dai-dai lokacin da aka kwashe kwanaki 60 da cikin dokar.
Hadiza ta ce, kara wa’adin dokar bai rasa nasaba da irin karin shirye-shirye da jihar ke yi na sake bude harkokin yau da kullum, da kuma bada cikakkiyar kariya ga al’ummar jihar.
A karshe mataimakiyar gwamnan ta kara da cewa, makarantu da wuraren ibada da kasuwanni za su ci gaba da kasancewa a rufe, yayin da za a rika tattaunawa da malamai da jami’an gwamnati da masarautun gargajiya da kungiyoyin sufuri da sauran su.
You must log in to post a comment.