Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Gwamnatin Jihar Kaduna Za A Rufe Wasu Makarantun Kiwon Lafiya Da Asibitocin Kudi

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ayyana kudurinta na rufe dukkanin kwalejojin kiwon lafiya da asibitocin kudi da ba su da rajista a jihar.

Kwamishinar Lafiyar Jihar Kaduna, Dokta Amina Baloni, ta ce ma’aikatarta ta riga ta fara bincike domin gano makarantun koyon aikin kiwon lafiya marasa rajista a jihar.

Ta ce a yanzu akwai sama da asibitoci 1,000 masu rajista da ma’aikatar lafiya ta jihar, amma duk da haka akwai wasu da dama marasa rajista.

Dokta Baloni ta ce akwai sharuda da ya kamata a bi kafin bude makarantun kiwon lafiya, wadanda ta ce matukar ba a cika su ba to za a rufe makarantar da aka kama.

Tace ba wai “Don kawai mutum yana da lasisin zama likita shi ke nan ya samu dammar bude kwaleji ko kuma asibiti ba, hakan ya sabawa doka.

Daga karshe ta shawarci iyaye da su guji tura ’ya’yansu makarantun kiwon lafiya na kudi domin mallakar shaidar karatu ta bogi.

Exit mobile version