Home Home Gwamnatin Borno Za Ta Ɗauki Malamai 5,000 Aiki Da Dawo Da Karatun...

Gwamnatin Borno Za Ta Ɗauki Malamai 5,000 Aiki Da Dawo Da Karatun Yamma

93
0

Gwamnar jihar Borno Babagana Zulum, ya ce za a dauki malamai dubu biyar aiki domin fara karatun firamare da sakandare da rana, a wani mataki na magance matsololin cunkoso da kuma rage yawan yaran da ba su zuwa makaranta.

Zulum ya bayyana haka ne a Maiduguri, yayin da ya ke jawabi bayan rantsar da shi a karo na biyu.

Ya ce duk da cewa sun gina sabbin makarantu masu girman gaske tare da fadada makarantun da ake da su da sabbin azuzuwa akalla dubu daya, amma har yanzu su na fuskantar matsalar cunkoso a azuzuwa, kuma su na fama da matsalar da dubban yaran da ba su zuwa makaranta.

Gwamna Zulum, ya ce nan ba da jimawa ba jihar Borno za ta fara tsarin makarantun firamare da sakandare na rana, don haka ya kafa kwamitin da zai tsara hanyoyin da za a fara karatun makarantun yamma, kuma zai tantance makarantun gwajin da za a zabo daga wasu manyan makarantun Maiduguri da ke da lantarki.

Zulum ya kara da cewa, bullo da tsarin karatun yamma zai bukaci karin ma’aikata, don haka ya umurci ofishin shugaban ma’aikata ya zakulo kwararrun ma’aikatan da a halin yanzu ba su aiki a sakatariyar gwamnati, wadanda za a horar da su a kan sanin makamar aikin.

Leave a Reply