Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar sake kwato kamfanin rarraba wutar lantarkin Najeriya, wanda aka fi sani da ‘NEPA’ daga hannun yan kasuwa domin ceto Najeriya daga matsanancin matsalar wuta da ake fama da shi.
Wannan mataki da gwamnati ke shirin dauka ya zo ne a daidai lokacin da za’a gudanar da cikakken nazari na karshe game da ayyukan kamfanonin rarraba wutar lantarki na DISCOS, domin tabbatar da da cewar suna aikinsu yadda ya kamata ko akasin haka.
Sai dai gwamnatin tarayya za ta biya ‘yan kasuwan da suka mallaki kamfanonin guda 10 kudi da yawansu ya kai Dala biliyan 2 da milliyan 4, kwatankwacin naira naira biliyan 736 a matsayin kudin fansa.