Home Coronavirus Gwamnati Ta Umarci Ma’aikata Daga mataki na 14 Zuwa Sama Su...

Gwamnati Ta Umarci Ma’aikata Daga mataki na 14 Zuwa Sama Su Koma Aiki

404
0
Gwamnati Ba Ta Cire Dokar Hana Zirga-Zirga A Tsakanin Jihohi Ba
Gwamnatin Tarayya ta fara aikin sake gina makarantun da Boko Haram su ka ragargaza a Jihar Yobe da sauran sassan jihohin Arewa maso Gabas.

Gwamnatin tarayya ta umarci ma’aikatan gwamnati daga mataki na 14 zuwa sama su koma bakin aikin daga ranar Litinin 4 ga watan Mayu.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarda da shugabar ma’aikatan tarayya Folashade Yemi-Esan ta fitar, tare da cewa an yi feshi a sakateriyar tarayya, kuma ana kokarin yi a sauran ofisoshin gwamniti.

Idan dai ba a manta ba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana a wajaban sa cewa, za a bi komai a hankali ta hanyar bin mataki daban-daban wajen sassauta dokar hana walwala, matakin da ya sa aka umarci ma’aikata daga mataki na 14 zuwa sama su koma bakin aiki.

Sai dai sanarwar ta ce, za a bude ofisoshin ma’aikata sau uku a mako, ma’ana a ranakun Litinin da Laraba da Juma’a, kuma za a rika tashi ne da karfe 2 na kowacce rana.

Haka kuma, sanarwar ta shawarci ma’aikatan su kayyade yawan bakin da za su rika karba a kowacce rana, sannan za a samar da sinadaran wanke hannu a daukacin ofisoshin.