Home Labaru Gwamnati Ta Kara Kuɗin Lambar Mota Da Lasisin Tuki A Najeriya

Gwamnati Ta Kara Kuɗin Lambar Mota Da Lasisin Tuki A Najeriya

161
0
Gwamnati Ta Kara Kuɗin Lambar Mota Da Lasisin Tuki A Najeriya

Gwamnatin tarayya ta yi ƙarin kuɗin Lambar mota da na lasisin tuki da kashi 50 cikin 100 a faɗin Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar bayan kammala wani taron masu ruwa da tsaki a fannin kula da tittuna da tuki wanda ya gudana a jihar Kaduna.

Acewar sanarwar, daga yanzu ‘yan Nijeriya za su rika biyan naira dubu 18 da 750 maimakon naira dubu 12 da 500 da ake biya a baya, a matsayin kuɗin lambar motar kansu da kuma ta haya, yayinda kuma za a rika biyan naira dubu 200 a matsayin kudin lamba ta musamman maimakon naira dubu 80 da ake biya a baya.

Lambar babur kuma za ta koma naira dubu 5 maimakon naira dubu 3 da ake biya a baya, yayinda lambobin musamman na gwamnati ta kamo dubu 20 daga dubu 15wanda hakan ke nuna cewa da wannan sabon tsarin karin ya kasance kashi 50 cikin 100.

Sanarwar ta kara da cewa, lasisin tuki na shekara uku ya koma dubu 10 daga dubu 6, ban da kuɗaɗen da banki ke caji, inda kuma lasisin shekara 5 ya koma dubu 15 daga dubu 10, yayinda lasisin masu tuka babur na shekara uku ya koma dubu 5 daga dubu 3, sai kuma lasisin shekara 5 da ya koma naira dubu 8 daga naira dubu 5.