Home Labaru Gwamnati Ta Haramta Hake-Haken Ma’adai A Jihar Zamfara

Gwamnati Ta Haramta Hake-Haken Ma’adai A Jihar Zamfara

558
0

Gwamnatin tarayya ta hana ci-gaba da duk wani aiki na hako ma’adanai a fadin jihar Zamfara, kamar yadda shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Muhammad Adamu ya bayyana wa manema labarai.

Gwamnatin tarayya dai ta sanar da cewa, an dakatar da duk wani aiki da ya shafi hako ma’adanai sakamakon yadda rikici ke faruwa a fadin jihar.

Muhammdd Adamu ya bayyana umarnin gwamnatin tarayya ne, yayin da ya ke ganawa da manema labarai na fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ya ce gwamnati ta gano cewa, akwai alaka tsakanin masu kai hare-hare da masu hako ma’adanai a boye, wanda sau tari hakan ke haifar da matsaloli da dama, don haka gwamnati ta umarci daukacin ‘yan kasar waje da ke hako ma’adanai su bar yankunan da ke dauke da arzikin gwal da sinadarin karafa.

Daga cikin wadanda su ka halarci taron tabbatar da wannan mataki kuwa akwai shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa Abba Kyari, da Daraktan hukumar tsaro ta DSS Yusuf Bichi da shugaban hukumar leken asiri ta kasa Ahmed Rufai.

Leave a Reply