Gwamnatin ta ja hankalin ‘yan ƙasa su rage yawan shan gishiri domin kariya daga cutuka da ke saurin kisa.
Ministan lafiyar, Farfesa Muhammad Ali Pate ya yi gargaɗin a ranar Talata lokacin bikin makon taƙaita shan gishiri a Abuja.
Ministan ya ce shan gishiri fiye da kima na da illa ga rayuwar dan’adam inda yake ta’azzara cutar hawan jini wadda ke haddasa bugun zuciya da shanyewar ɓarin jiki.
Ya ƙara da cewa shan gishiri fiye da kima a Najeriya babban abu ne da ke taimakawa da kaso 10 na mace-macen da ake yi a ƙasa.














































