Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Gwamnan Ondo Akeredolu Ya Mika Ragamar Mulki Ga Mataimakin Sa

Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu, ya mika ragamar
mulki ga mataimakin sa Lucky Aiyedatiwa saboda tsananin
rashin lafiyar da ya ke fama da shi.

Akeredolu dai ya aike da wasikar haka ne ga majalisar dokoki ta jihar domin ya sanar da su halin da ya ke ciki.

Gwamna Akeredolu, ya ce zai koma bakin aiki ranar 6 ga watan Yuli bayan ya samu sauki kuma ya kammala hutun da ya ke yi a kasar waje.

Rotimi Akeredolu dai ya kwana biyu ba a gan shi a ofishin sa ba, inda aka rika yada jita-jitar cewa ya rasu ne ko kuma ya na cikin tsananin rashin lafiya.

Exit mobile version