Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Gwamnan Katsina Ya Sha Alwashin Shiga Daji Domin Sulhu Da Masu Kai Hare-Hare

Gwamnan Katsina Ya Sha Alwashin Shiga Daji Domin Sulhu Da Masu Kai Hare-Hare

Gwamnan Katsina Ya Sha Alwashin Shiga Daji Domin Sulhu Da Masu Kai Hare-Hare

Gwamnatin jihar Katsina ta ce za ta tattauna da mutanen da ake zargi da kai hare-hare da satar mutane domin kudin fansa don kawo karshen matsalar tsaro da take addabar jihar.

Karanta Wannan: Matakan Tsaro: Jami’an ‘Yan Sanda Sun Kama Kayan Hada Bom A Birnin Abuja

Daraktan yada labaran gwamnan jihar, Audu Labaran, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai, ya a wannan karon gwamna Aminu Bello Masari zai shiga daji domin tattaunawa da maharan.

Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan harkar tsaro da aka yi a fadar gwamnatin ta Katsina.

Wannan dai na zuwa ne ‘yan kwanaki kadan bayan wasu mahara sun akfkawa garin Wurma a karamar hukumar Kurfi, inda aka sace mata da dama.

Wadanda suka halarci taron sun hada da gwamna da mataimakinsa da sakataren gwamnati da Sarkin Katsina da shugabannin hukumomin tsaro da shugabannin kungiyoyin Fulani da kuma wasu masu kai hare-haren da suka ce sun tuba.

Exit mobile version