Home Labaru Gwamnan Jihar Ebonyi Ya Yi Barazanar Kama Iyayen Ƴan Awaren Biyafara

Gwamnan Jihar Ebonyi Ya Yi Barazanar Kama Iyayen Ƴan Awaren Biyafara

20
0

Gwamnan jihar Ebonyi David Umahi, ya yi barazanar kama iyayen ƴan awaren da ake zargi da kai hari kan fararen hula.

Gwamnan ya ce matakin na zuwa ne sakamakon karuwa yawan tashin hankalin da ake yi yanzu a jihar ta Ebonyi.

Umahi ya ce sarakunan gargajiya sun san ƴan bindigar da ke kai hare-haren da iyayen su da kuma maboyarsu amma sun ƙi tona su.

Yankin kudu maso gabashin kasar nan dai na fama da tashin hankali, wanda kuma ke da alaƙa da ƴan aware masu fafutukar kafa ƙasarsu ta Biyafara.