Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen gwamnan jihar Imo, ta tabbatar da nasarar Hope Uzodimma a matsayin halastaccen gwamnan jihar.
Kotun wadda ta yanke hukuncin a Abuja, ta yi watsi da ƙorafin jam’iyyar LP da ɗan takarar ta, Athan Achonu da suka shigar da ƙara suna ƙalubalantar nasarar Uzodimma.
A hukuncin da alƙalan kotun uku ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay suka yanke, sun ce zaɓen da aka yi wa Uzodimma an yi shi ne bisa doron dokar zaɓen ƙasa.
Haka kuma kotun ta ce jam’iyyar LP ta gaza gabatar da hujjoji kan zarge-zargen da ta yi na aringizon ƙuri’u da rashin bin ƙa’idar dokar zaɓen.