Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Gwamnan Bauchi: Jam’iyyar PDM Ta Janye Karar Da Ta Shigar

Jam’iyyar PDM ta ce ta janye karar da ta shigar a gaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Bauchi, wacce take kalubantar nasarar da Sanata Bala Muhammad, ya samu na zama gwamnan jihar a babban zaben 2019.

kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Bauch

Jam’iyyar ta janye karar ne a zaman da kotun ta gudanar a Asabar dinnan, inda Lauyan jam’iyyar ya shigar da bukatar neman kotun ta amince musu janye karar da suke yi akan gwamnan jihar Bauchi, da jam’iyyar PDP, da kuma hukumar zabe ta INEC.

Da yake sallamar karar daga gaban sa, shugaban kotun sauraron kararrakin zaben jihar, Justice Salihu Shuaibu, ya shaida cewar ya sallami karar ne bayan bukatar janye karar da Lauyan jam’iyyar PDM ya shigar.

A ganawar sa da ‘yan jarida bayan fitowar su daga kotun, Lauyan jam’iyyar PDM Barista Aliyu Lemo, ya ce sun janye karar da suke yi din ne domin su ba gwamna Bala Muhammad cikakken dama da ikon ci gaba da gudanar da aiyukan raya jihar ta Bauchi.

Ya ce, ‘ya’yan jam’iyyar su sun tabbatar musu da cewar gwamna Bala Muhammad, ya zo da kyawawan manufofi na kyautata jihar da samar da ababen more rayuwa wa al’ummar. 4j0Ir8M��xI

Exit mobile version