Home Labaru Ilimi Gwamna Ya Kori Shugabannin Makarantun Sakandare 7

Gwamna Ya Kori Shugabannin Makarantun Sakandare 7

13
0
Screenshot 2024 02 04 10.22.37 AM
Screenshot 2024 02 04 10.22.37 AM

Gwamnatin jihar Taraba ta dakatar da wasu shugabannin makarantun sakandare bakwai bisa zargin yin zagon kasa ga ilimi a jihar.

Ma’aikatar ilimi ta jihar ta ce shugabannin makarantun suna karbar kudi daga hannun dalibai wanda ke kawo cikas ga shirin Gwamna.

Kwamishiniyar ilimi ta jihar, ce ta sanar da dakatar da shugabannin makarantun guda bakwai a cikin sanarwa da ta fitar,

Misis Augustina Yahaya ta ce dukkanin wadanda abin ya shafa sun aikata laifuffukan da nufin kawo cikas ga nasarorin da aka samu a shirin ba da ilimi kyauta da gwamnan ya bayyana.

Sauran shugabannin makarantun da gwamnatin ta dakatar sun hada da na shugaban makarantar GDSS Kofai da Salihu Dogo a Jalingo.

An kuma kori shugabannin makarantun GDSS Kununi, GDSS Jouro Yinu, GDSS Kakulu, da kuma GDSS Yakassai da ke a Wukari.

Leave a Reply