Home Labarai Gwamna Wike Ya Maida Zazzafan Martani Ga Ministan Buhari Mai Murabus

Gwamna Wike Ya Maida Zazzafan Martani Ga Ministan Buhari Mai Murabus

162
0

Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers, ya bayyana tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi a matsayin wanda ya kai maƙurar gazawa.

Da ya ke jawabi yayin kaddamar da ginin tsohon Bankin Inshora na Riv da gwamnatin sa ta Sabunta a Fatakwal, Wike ya zargi tsohon ministan da gaza taɓuka wa al’ummar jihar rives komai a tsawon shekaru 7.

Ya ce mutumin da ya gaza kawo ayyuka a jihar sa, abin da ya kamace shi kawai ya rufe fuskar sa saboda kunya, sannan ya daina tsoma baki a harkokin siyasar Rivers.

Gwamnan Wike ya bayyana haka ne, yayin maida martani a kan kalaman Rotimi Ameachi, wanda ya ce gwamnatin jihar Rivers ba ta kyauta ba wajen rashin gudanar da Jana’izar marigayi Chief Alabo Tonye Graham-Douglas.

Wike ya bugi ƙirjin cewa, lokacin ya na ƙaramin Ministan, ya sa an gina tsangayar koyar da ilimin shari’a a Jami’ar Fatakwal, sannan aka gina Oil And Gas Poly a Bonny.

Leave a Reply