Sabon gwamnan Jihar Katsina Dakta Dikko Umar Raɗɗa, ya
yi sabbin naɗe-naɗen da su ka haɗa da Sakataren Gwamnati
da Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar da Daraktan
Yaɗa Labarai da sauran su.
A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Gwamna Raɗɗa ya naɗa Ahmed Musa Ɗangiwa a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, yayin da Alhaji Jabiru Tsauri ya zama Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati, sai kuma Barista Muhtar Aliyu Saulawa da aka nada a matsayin mataimakin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, da Alhaji Abdullahi Aliyu Turaji a matsayin Babban Sakataren Ofishin Gwamna.
Sauran sun hada da Malam Maiwada Ɗan Malam a matsayin Babban Daraktan Yaɗa Labarai, da Ibrahim Kaula Mohammed a matsayin Babban Sakataren Yaɗa Labarai.
Gwamna Dikko Radda, ya kuma naɗa Alhaji Bishir Maikano a matsayin Babban Mataimaki na Musamman a kan Tsare- tsaren fadar gwamnati.
Dikko Raɗɗa, ya taya waɗanda naɗin ya shafa murna, sannan ya bukaci su hada kai da shi domin ganin an dawo da martabar jihar Katsina.
You must log in to post a comment.