Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Gwamna Ortom Na Jihar Benue Ya Ce Ya Yafe Wa Shugaba Buhari

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, ya ce ya yafe wa Shugaba Muhammadu Buhari a kan duk takkadamar da ta shiga tsakanin su a baya.

Samuel Ortom ya bayyana haka ne, ya yayin wata hira da ya yi a cikin shirin The Morning Show na gidan talabijin na Arise.

Gwamna Ortom dai ya kasance ya na sukar fadar shugaban kasa, a kan yadda ya ce gwamnatin tarayya ta na sukar gwamnatin sa a kan kashe-kashen da ake yi a jihar sa. Samuel Ortom, ya kuma shawarci shugaba Buhari ya tsaya domin taimaka wa sabuwar gwamnatin Bola Tinubu don a ciyar da kasa da ma jihar sa gaba

Exit mobile version