Home Labaru Gwamna Matawalle Ya Ce Ba Sauran Sulhu Da ‘Yan Bindiga Sai Kisa

Gwamna Matawalle Ya Ce Ba Sauran Sulhu Da ‘Yan Bindiga Sai Kisa

169
0
Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya ce 'yan bindiga sun yi watsi da damar da suka samu ta sulhu a baya, yanzu tsakanin gwamnati da su sai aikawa lahira.

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya ce ‘yan bindiga sun yi watsi da damar da suka samu ta sulhu a baya, yanzu tsakanin gwamnati da su sai aikawa lahira.

Cikin wani bidiyo da ke ta yawo a kafafen sada zumunta, an ga Gwamna Matawalle yana jawabi a wani masallaci bayan idar da sallah, inda yake yi wa al’umma bayani kan halin da ake ciki a jihar.

Matawalle ya ce “gaskiyar magana suna shan wuta sosai, ko jiya an turo kwamiti babba a sameni, cewa in tsagaita don Allah, in saki a rika samun abinci na ce wallahi ba zan saki ba,.

Duk wani abu da Allah ya ce muyi munyi, saboda haka mun yi iyakar yinmu, yanzu abin da muke yi shi ne mu sada su da ubangijinsu su amsa tambayoyi ga Allah.”

Leave a Reply