Home Labarai Gwamna Diri Ya Ce An Fi Samun Zaman Lafiya A Mulkin Jonathan

Gwamna Diri Ya Ce An Fi Samun Zaman Lafiya A Mulkin Jonathan

87
0

Gwamnan jihar Bayelsa Douye Diri, ya koka da yadda sha’anin tsaro ya kara tabarbarewa a Nijeriya, ya na mai cewa an fi samun kwanaciyar hankali kafin APC ta karbi mulkin kasar nan.

Da ya ke jawabi a birnin Yenagoa, Douye Diri ya shaida ma
wasu manyan jami’an tsaro cewa batun tsaro ya tabarbare a
yankin Arewa.

Ya ce kashe-kashen da ake yi a jihohin Arewa sun shafi yankin
kudu, lamarin da ya ce ya na maida Nijeriya baya.

Gwamna Diri ya kara da cewa, abubuwa sun fi muni yanzu a
kan shekara ta 2015, don haka wajibi ne gwamnatin tarayya ta
kara kokarin da ta ke yi game da matsalar tsaro, idan bah aka ba
talakawa za su koya masu hankali domin sun san abin da ya
kamata su yi a shekara ta 2023.

Leave a Reply