Home Labarai Gwamantin Kano Ta Hana Tsohon Sarki Aminu Ado Dawo Wa Jihar

Gwamantin Kano Ta Hana Tsohon Sarki Aminu Ado Dawo Wa Jihar

79
0
Abba Kabir Yusuf Governor Kano State (1)
Abba Kabir Yusuf Governor Kano State (1)

Gwamanti jihar  Kano ta dakatar da yunƙurin da tsohon sarki Aminu Ado Bayero ya yi na dawo wa jihar

kafin wa’adin sa’a 48 da gwamnatin ta gindaya wa duk sarakunan da aka tsige.

Rahotanni sun ce, Aminu Ado ya je garin Ijebu-Ode, da ke Ogun ne domin ganin Oba Sikiru Adetona,

na Masarautar Ijebu domin neman shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da yunƙurin tsige shi.

Sai dai wani rahoto ya tabbatar da cewa, gwamnatin Kano ta samu labarin yunƙurin tsohon sarkin na dawo wa Kano, nan da nan,

ta sanar da jami’an tsaro domin su hana shi shigo wa jihar a wani dalili na tsaro da zaman lafiya.

Wata majiya ta tabbatar da cewa, an hangi motocin fadar sarki a filin jirgin saman  Kano suna tsumayin dawowar tsohon sarkin amma daga baya aka umarce su su koma Fada.

tuni majalisar ta rushe dokar da ta kafa Masarautun Kano guda biyar da suka haɗa da Kano,Bichi, Rano,Karaye da Gaya

da aka yi a shekara ta 2019 kuma gwamnan Abba Kabir Yusuf ya sanyawa hannu.

Tuni gwamnan ya bayyana sunan Muhammadu Sanusi II a matsayin wanda ya dawo masarautar ta  Kano a karo na biyu.

Leave a Reply