Home Labaru Gurbatawa Muhalli: Kamfanin Shell Zai Biya Ƴan Najeriya Diyyar Dala Miliyan 111

Gurbatawa Muhalli: Kamfanin Shell Zai Biya Ƴan Najeriya Diyyar Dala Miliyan 111

59
0

Kamfanin Shell zai biya ƴan Najeriya da ya gurbatawa muhalli cikin shekaru sama da 50 Diyyar Dala miliyan 111.

Kamfanin ya ce gurbacewar muhallin ya faru ne ta hanyar mutanen da yake mu’amala dasu.

Kakakin kamfanin ya ce kuɗaɗen da za su biya zai warware takaddama tsakaninsa da Al’ummar Ejama-Ebubu kan gurbata musu muhalli a lokacin yakin Biafara tsakanin 1967 zuwa 1970.

A shekara ta 2010 ne dai kotun Najeriya ta ci kamfanin na Shell tarar Dala Miliyan 41.36 inda kamfanonin ya yi ta daukaka kararaki.