Wata mahaukaciyar guguwa dauke da ruwan sama ta nufi kasar Mozambique wata daya bayan da makamanciyar ta ta haddasa mummunar barna da kashe mutane da dama a kasar.
Sabuwar guguwar da masana suka sanya wa suna Kenneth, ta nufi gabar ruwan arewa maso gabashin kasar ne, bayan da ta yi mumman ta’adi a Tsibirran kasar Comoros.
Hukumar kula da hasashen yanayi ta Faransa ta yi gargadin cewa, guguwar za ta iya haddasa tumbatsar teku har da mamaye gidaje da gonaki a kasar ta Mozambique.