Home Labaru Gudanar Da Mulki: Gwamnatin Tarayya Ta Hada Hannu Da Wani Kamfani

Gudanar Da Mulki: Gwamnatin Tarayya Ta Hada Hannu Da Wani Kamfani

209
0

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da aiki da kamfanin Galazxy Backbone a tsarin zamanantar da aikin gwamnati ta hanyar yanar gizo.

Mustapha ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce a shirye gwamnati take ta yi maraba da zuba jari akan abubuwan da suka shafi fasahar zamani.

Ya ce jajircewa da kuma yin abubuwan da suka kamata zai taimaka wajen cika burin gwamnati na zamanantar da aikace-aikacen ta.

Mustapha ya kara da cewa horas da ma’aikatan gwamnati da dama a harkar zai taimaka wajen gudanar da ayyuka yadda ya kamata a bangarorin da abin ya shafa.

Ya ce kamfanin ya shahara kuma ya samar da yanayi mai kyau, tare da cin nasara a duk wasu abubuwa da ya sanya a gaba da suka shafi aikace-aikacen yanar gizo a Najeriya.

A nasa jawabin shugaban kamfanin Yusuf Kazaure, ya ce kamfanin ya kafa aikace-aikacensa a jihohi 11 cikinsu harda babban birnin tarayya Abuja.

Leave a Reply