Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Goyon Baya: Zanga-Zanga Ta Barke A Yamai Bayan Juyin Mulki

Ɗaruruwan mutane ne suka yi cincirindo a gaban ginin majalisar Nijar da ke Yamai, domin nuna goyon baya ga sojoji.

Masu zanga-zangar sun buƙaci Rasha ta kawo masu ɗauki, tare da roƙon dakarun tsaron Faransa da su janye daga ƙasar.

Wasu masu zanga-zangar na ɗauke da tutar Rashar, Sai dai har yanzu babu wata alama da ke nuna wani yunƙurin shiga tsakani da Rasha ta yi.

Masu zanga-zangar sun cinna wa ofishin jami’iyar PNDS Tarayya wuta, wadda kuma ita ce jam’iyar hamɓarraen shugaban ƙasar.

Ra’ayoyin ƴan ƙasar dai ya banbanta, inda wasu ke ganin juyin mulkin abu ne marar kyau, wasu kuma na ganin matakin ya yi daidai.

Exit mobile version