Home Labaru Gobarar Daji: Mutane 42 Suka Hallaka A Algeria

Gobarar Daji: Mutane 42 Suka Hallaka A Algeria

135
0

An tabbatar da mutuwar mutane akalla arba’in da biyu a kasar Algeria, sakamakon gobarar daji daban-daban fiye da dari daya.

Mafiya munin gobarar na ci ne a tsaunuka masu kurmi a yankin Kabylie, inda sojoji ashirin da biyar suka mutu yayin da suke ƙoƙarin kashe wuta.

An bayyana, cikin hotuna na wayar salula, ana iya ganin mutane na gudu don tserewa daga gobarar wadda ke tunkarar garuruwa da kauyuka a yankin Kabylie.

Shugaban Algeria, Abdelmajid Tebboune, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su yana mai cewa sojojin sun ceto mutane fiye da dari daya daga gobarar.

Leave a Reply