Home Home Gobara Ta Ƙona Rumbun Adana Magunguna A Gombe

Gobara Ta Ƙona Rumbun Adana Magunguna A Gombe

137
0

Wata gobara ta ƙona rumbun adana magunguna a jihar Gombe.

Gobarar wadda ta tashi da asubahin jiya Litinin, ta lalata miliyoyin allurai tare da janyo rasa kayayyaki na biliyoyin naira.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Ibrahim Uba Misilli ya fitar, ta ce ta ce rumbun na ɗauke da alluran riga-kafin cutar shan-inna sama da miliyan biyu da kuma sauran magunguna.

A ziyara da ya kai wurin da abin ya faru, gwamna Inuwa Yahaya ya nuna damuwarsa, inda ya ce hakan babban koma-baya ne ga jihar ta Gombe, musamman ma a daidai lokaci da ta ke shirin kaddamar da fara riga-kafin polio a watan Maris.

Gwamnan ya yi kira ga ƙungiyoyin ba da agaji da masu ruwa da tsaki a ɓangaren lafiya da su kawo wa jihar ɗauki, inda ya nanata rawar da rumbun ke taka wa wajen tallafawa ɓangaren lafiya ba ga jihar kaɗai ba har ma faɗin arewa maso gabas.

Sauran kayayyaki da gobarar ta ƙona sun haɗa da na’urorin firji, da silinda, na’urorin sanyaya ɗaki da kuma babura.

Leave a Reply