Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bi sahun shugabanni da al’ummar duniya wajen jajanta wa al’umma da gwamnatin Indosnesiya bisa iftila’in girgizar ƙasar da ta auku a yammacin ƙasar.
Rahoyanni sun tabbatar da cewa Girgizar ƙasar ta kashe fiye da mutum 160, tareda lalata gidaje akalla 2,200 inda mutum 13,000 suka rasa gidajen su a lardin Java.
A wani sako da mataimaki na musamman ga shugaban ƙasar malam Garba Shehu ya fitar, shugaba Buhari ya ce a madadin al’ummar Najeriya yana mika sakon jaje zuwa ga gwamnati da al’ummar Indonesiya kan iftila’in.
Buhari ya ƙara da cewa ”Najeriya na tare da wadanda lamarin ya shafa kuma ana sane da mawuyacin halin da suka shiga”.