Jam’iyyar APC ta jihar Kano ta zargi shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado da izgilanci wajen kama tsohon kwamishinan ayyuka na jihar da ya yi.
Kakakin jam’iyyar APC na jihar Kano Ahmed Aruwa ya bayyana haka, bayan kotu ta tura Injiniya Wada Saleh zaman waƙafi har zuwa ranar 14 ga watan Yuli bisa zargin badaƙalar Naira biliyan guda ta gyaran hanyoyi.
Ahmed Aruwa, ya ce tun farko jam’iyyar APC ta san za a yi haka, saboda Rimin Gado ya na da burin burge shugabannin da su ka ɗora shi a kan muƙamin da ya ke a kai yanzu.
Ya ce Rimin Gado ya faɗa da bakin sa cewa zai gayyaci Gwaggo da Abba, don haka an fara ne, kuma so ake a tabbatar wa da duniya wadannan abubuwa da ake so a yi.
Aruwan ya kara da cewa, tsohon gwamna Ganduje zaɓaɓɓe ne, kuma a wancan lokacin da ya ke bada umarni da jan biro hukuncin da ya zaɓe shi ne ya ba shi wannan dama.
A karshe ya gargaɗi Barista Rimin Gado cewa jam’iyyar APC za ta iya bincikar sa duk lokacin da ta dawo a kan karagar mulkin jihar Kano.