Home Labaru Gaskiyar Lamari: Shakatawa Ce Ta Kai Ni Amurka Ba Jinya Ba —...

Gaskiyar Lamari: Shakatawa Ce Ta Kai Ni Amurka Ba Jinya Ba — Gwamna Sule

338
0

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, ya musanta zargin da ake yi masa na cewa a yanzu haka ya fita neman magani ne a Kasar Amurka, yana mai jaddada cewa ya ziyarci Amurkan ne domin ganin ’ya’yan sa a yayin da yake hutunsa na shekara.

Ya yi wannan karin haske ne a yayin da ya bayyana a matsayin bako a wani shiri da gidan talbijin na Channels.

Gwamnan wanda ya dauki zargin da ake yi masa a matsayin raha, ya yi bayanin cewa ya saba tafiya hutu duk karshen shekara a watan Disamba, kuma yana amfani da wannan dama ya ziyarci iyalin sa a garin Houston na Jihar Texas da ke Amurka.

Gwamna Sule ya ci gaba bayar da bayanin cewa, a yayin da yake hutu a Amurka kamar yadda ya saba tun a baya, yana kuma amfani da wannan dama ya rika zuwa ana bincikar lafiyar sa lokaci zuwa lokaci.

Leave a Reply