Home Labaru Gasar Zakarun Turai: Madrid Ta Haye Zagayen Daf Da Ƙarshe Bayan Doke...

Gasar Zakarun Turai: Madrid Ta Haye Zagayen Daf Da Ƙarshe Bayan Doke City

63
0
gun 1381310671 uefa champions league
gun 1381310671 uefa champions league

Real Madrid da Bayern Munich sun bi sahun Paris Saint Germain da Brusia Dortmund zuwa wasan daf da ƙarshe na gasar zakarun Turai ko Champions League.

Real Madrid ta dauki fansa kan Manchester City da ci 4-3 a bugun fanariti, bayan da ta shi wasa 1-1 a Etihad daren Laraba.

Rodrygo ne ya fara ci wa Madrid ƙwallo a mintuna 12 da soma wasa kafin Kevin De Bruyne farke wa City a mintuna 76 aka ƙarkare kunnen doki 1-1, wato 4-4 jimilla gida da waje, abin da ya sa aka je ƙarin lokaci, har aka kai bugun finareti.

Sai dai mai tsaron ragar Real Madrid Andriy ya kawo ƙarshen bajintar da masu rike da kambin City suka nuna amatsayin mafi tsaron baya na gasar bayan tare ƙwallayen Bernardo Silva da Mateo Kovacic a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Mai tsaron ragar Madrid Ɗan kasar Ukraine, wanda ya maye gurbin Thibaut Courtois da ya ji rauni a kakar wasa ta bana, ya fanshi kansa ne kan kura kurai da ya tafka a haduwarsu ta farko da aka tashi 3-3 a Spain.

Tun shekarar 2018 City ba ta yi rashin nasara a gida ba a gasar cin kofin zakarun Turai, amma masu rike da kofin har 14 sun karya wanna tarihi saboda jajircewar da suka yi a daren jiya, duk da yunkuri City na saita kwallo har sau 34.

Da wannan mataki Madrid za ta kara da Bayern Munich a wasan daf da ƙarshe bayan da ƙungiyar ta Jamus ta doke Arsenal da ci 3-2.

Bayern Munich ta kai daf da ƙarshe ne bayan da ta doke Arsenal 1-0 a Allianze Arena – wato 3-2 kenan gida da waje.

Joshua Kimmich ne ya ci kwallon a mintuna na 63, wato bayan hutun rabi lokaci, da taimakon Raphael Guerreiro.

A zagayen farko ƙungiyoyin biyu sun tashi 2-2 a wasan da suka fafata ranar Talata a Emirates.

Leave a Reply