Home Labarai GASAR ZAKARU: BABU TABBACIN MBAPPE YA BUGA WASAN PSG DA BAYERN MUNICH

GASAR ZAKARU: BABU TABBACIN MBAPPE YA BUGA WASAN PSG DA BAYERN MUNICH

70
0

Yau ake dawowa wasannin gasar cin kofin zakarun Turai zagayen ‘yan 16, wato kungiyoyin da suka iya nasarar tsallakewa daga matakin rukuni inda a yau din za a gwabza tsakanin kungiyar Tottenham wadda za ta yi tattaki zuwa gidan AC Milan yayin da PSG za ta karbi bakoncin Bayern Munich.

Wasu bayanai sun ce dan wasan gaba na PSG Kylian Mbappe ya koma atiisaye a jiya litinin gabanin wasan da kungiyar ta sa za ta doka wanda ke bayar da fatar yiwuwar dan wasan ya iya taka leda a karawar ta yau.

Mai horar da ‘yan wasan kungiyar ta PSG Christophe Galtier yayin wata tattaunawar sa a jiya litinin, ya ce bashi da tabbas kan yiwuwar ko dan wasan zai iya taka ledar.

A cewar Galtier Mbappe ya yi atisaye tare da ‘yan wasan PSG a jiya kuma alamu na nuna da karfi a jikin sa amma dole su jira abinda likitoci za su ce gabanin bashi dama.

A farkon watan nan ne Mbappe ya samu rauni a cinya wanda liktoci suka bayar da shawarar ya yi jinyar makwanni 3 gabanin dawowa filin wasa. 

Haduwarta ta yau dai za ta tunowa bangarorin biyu karawar su ta wasan karshe a gasar ta cin kofin zakarun Turai ta 2020 wadda PSG ta sha kaye da kwallo 1 mai ban haushi a hannun Bayern Munich.