Home Labaru Kiwon Lafiya Gasar Shan Kwaya: Mutum Daya Ya Mutu, Daya Ya Haukace

Gasar Shan Kwaya: Mutum Daya Ya Mutu, Daya Ya Haukace

983
0

Wadansu matasa mazauna garin Sabo Shagamu sun bi dare inda suka yi ta lalibe a burbushin miyagun kwayoyin da Hukumar Kwastam da hadin gwiwar Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna NAFDAC, suka kone a karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Hukumar Kwastam Aminu Dahiru.

Hukumomin biyu sun kone miyagun kwayoyin da Hukumar Kwastam ta kama ne da aka kiyasta kudinsu kan sama da Naira biliyan 14.

                                                                                                                                               Miyagun kwayoyin da suka hada da tiramadol da dangoginta cike a kwantaina 58 an yi aikin kone su cikin kwana biyu a dandalin kone kayayyaki irin wadannan a hanyar Ikorodu daga garin Shagamu a Jihar Ogun.

Matasan mazauna garin Sabo Shagamu sun bi dare ne a ranar Juma’a suka yi ta lalube a burbushin miyagun kwayoyin suka kai ga wadanda ba su gama konewa ba suka yi ta jida suka tafi da su Shagamu suka yi gasar shan kwayar tiramadol.

Malam Abdullahi Muhammad Alkwatanawi, mazaunin garin Shagamu ya shaida cewa matasan su uku ’yan ci-rani ne da suka zo garin Shagamu daga Arewa, Biyu daga cikinsu daga Jihar Sakkwato, yayin da ga jihar Kebbi.X!wQ��N�9I�

Leave a Reply