Home Home Gasar Premier:  Arsenal Za Ta Ci Gaba Da Jan Ragamar Teburi Har...

Gasar Premier:  Arsenal Za Ta Ci Gaba Da Jan Ragamar Teburi Har Zuwa Kirsimeti

177
0

Arsenal za ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin gasar Premier har zuwa lokacin bikin Kirsimetin 2022 a karon farko tun bayan 2007.

Gunners ta yi nasarar doke Woverhampton da ci 2-0 a wasan mako na 16 a babbar gasar tamaula ta Ingila da suka fafata ranar Asabar a Molinuex.

Kyaftin din Arsenal, Martin Odegaard shi ne ya ci kwallayen, bayan da suka sha ruwa suka koma fafatawar zagaye na biyu.

Da wannan sakamakon Gunners ta bai wa Manchester City ta biyu tazarar maki biyar, bayan da City ta yi rashin nasara 2-1 a hannun Brentford a Etihad.

Kungiyar da Mikel Arteta ke jan ragama ta yi wasa 14 da cin 12 da canjaras daya da rashin nasara a fafatawa daya da maki 37.

Haka kuma kungiyar da take Emirates ta ci kwallo 33 an kuma zura mata 11 a raga kawo yanzu, tana cikin masu karancin kwallaye da aka ci a kakar nan.

Leave a Reply