Tawagar mata a gasar cin kofin duniya ta mata wato Super Falcons sun yi nasara a karawar da suka yi da Australiya, mai masaukin baƙi.
Najeriyar ta samu nasarar ce bayan ta zura wa Australiya ƙwallo uku, yayin da ƴan wasan na Australiya suka zura ƙwallo biyu.
Wasu daga cikin ƴan wasan na Najeriya sun ɓarke da kukan murna bayan da lafari ta hura usur na kammala wasan…
Ƴar wasan Australiya Emily van Egmond ce ta fara zura ƙwallo a minti na 45 bayan fara wasa yayin da Uchenna Kanu ta farke wa Najeriya bayan ƙarin lokaci ana dab da tafiya hutun rabin lokaci.
Bayan dawowa hutun lokaci ƴar wasan Najeriya Osinachi Ohale ta zura ƙwallon Najeriya ta biyu a minti na 65, Daga nan sai Asisat Ohoala ta cike wa Najeriya ƙwallo ta uku a minti na 72.
Sai dai ana dab da tashi wasan, a cikin ƙarin lokaci ƴar wasa Alanna Kennedy ta zura ƙwallo a ragar Najeriya hakan ya sa aka tashi wasan Australiya na da ƙwallo biyu yayin da Najeriya ke da uku.