Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Gasar Firimiya: Manchester City Ta Lallasa Arsenal Da Ci 5 Da Nema

Man U & Arsenal

Kungiyar Manchester City ta lallasa Arsenal da ci 5-0 a karawar da suka yi a gasar Firimiya ta Ingila, wanda shine kaye na 3 a jere da kungiyar Arsenal ta gani da bude fara sabuwar gasar bana.

Ilker Gundogan ya fara jefawa Manchester City kwallon ta a minti 7 kacal da fara wasan, yayin da Tores ya jefa ta 2 a minti 12, sannan Gabriel Jesus ya jefa ta 3 a minti 43 kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Ana dawowa daga hutun rabin lokaci Rodri ya jefawa Manchester City ta 4, sannan Torres ya jefa ta 5 a minti 84, abinda ya baiwa City damar komawa saman tebur da maki 6 kafin sauran wasannin na yau.

Yayin gudanar da wasan an baiwa dan wasan Arsenal guda Granit Xhaka jan kati saboda laifin da ya aikata, abinda ya rage yawan ‘yan wasan kungiyar.

Wannan shine karon farko da Arsenal ta kasa cin wasa a karawa uku da fara kakar Premier League tun bayan 1954/55.

City ta zama ta uku da ta zura kwallo 10 a raga a wasa biyu a gida da fara Premier League a kakar tamaula, bayan Arsenal da ta yi wannan bajintar a 2010/11 ta ci kwallo 10 da Manchester United da ta zura 11 a raga a 2011/12.

Tuni masu sha’awar kwallon kafa suka fara tsokaci dangane da makomar mai horar yan wasan Arsenal Mikel Arteta wanda ya gaza taka rawar gani tun bayan fara sabuwar kakar ganin yadda suka barar da maki 9 da kuma kasa jefa koda kwallo guda a raga.

Exit mobile version