Kungiyoyin da ke wasa a gasar firimiyar Ingila na iya kada kuri’ar jinkirta rufe kasuwar hada-hadar ‘yan wasa kafin fara gasar a taron su na 12 ga Satumba.
Shekaru biyu da suka gabata, kungiyoyin suka kada kuri’ar goyon bayan rufe kasuwar kafin a fara gasar sabuwar kaka, domin rage matsalar da ake samu a tawagogin kungiyoyin.
Sai dai saura kasashen ba su bi sahun kungiyoyin gasar firimiyar Ingila ba, saboda haka suna da damar sayen ‘yan wasa ko kuma karbar aron su a gasar firmiyar Ingila.
Kamar yadda kafofin yada labarai suka ruwaito, za a gudanar da taron shugabannin kungiyoyin gasar firimiya a mako mai zuwa, inda za su dauko wannan batun da nufin ganin kasuwar na ci daidai da sauran takwarorin su a Turai.
You must log in to post a comment.