Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Gasar Champions League: Ko Karim Benzema Zai Buga Wa Real Wasa Da Inter Milan Kuwa?

Real Madrid ta yi nasara a gidan Real Sociedad da ci 2-0 a wasan mako na 16 a gasar La Liga na ranar Asabar.

Real Madrid ta yi nasara a gidan Real Sociedad da ci 2-0 a wasan mako na 16 a gasar La Liga na ranar Asabar.

Real ta ci kwallon ta hannun Vinicius Junior a minti na biyu da komawa zagaye na biyu, sannan Luka Jovic ya ci na biyu.

A wasan ne golan Real Madrid ya yi wa kungiyar karawa ta 150, tun bayan da fara taka mata leda a ranar 1 ga watan Satumbar 2018.

Real Madrid wadda ke mataki na daya a kan teburin La Liga za ta buga wasan karshe a cikin rukuni da Inter Milan ranar Talata a Champions League.

Sai dai kawo yanzu ba a tabbaci ko Kraim Benzema zan buga fafatawar, wanda ake cewa watakila sai a karawa da Atletico Madrid zai buga wasa, bayan da ya ji rauni a wasan na ranar Lahadi a La Liga.

Dan kwallon Faransa ya fita daga wasan na La Liga a minti na 17 da fara tamaula, bayan da ya dunga dingisawa daga nan Luka Jovic ya canje shi.

Exit mobile version