Home Labaru Garkuwa Da Mutane: ‘Yan Sanda Sun Ceto Yan Bautar Kasa 4 Da...

Garkuwa Da Mutane: ‘Yan Sanda Sun Ceto Yan Bautar Kasa 4 Da Aka Sace A Hanyar Gusau

402
0
Garkuwa Da Mutane: ‘Yan Sanda Sun Ceto Yan Bautar Kasa 4 Da Aka Sace A Hanyar Gusau
Garkuwa Da Mutane: ‘Yan Sanda Sun Ceto Yan Bautar Kasa 4 Da Aka Sace A Hanyar Gusau

Jami’an ‘yan sandan Nijeriya sun samu nasarar ceto matasa masu yi wa kasa hidima su hudu da masu garkuwa da mutane suka sace a ranar Litinin.

Kakakin rundunar DCP Frank Mba ya bayyana hakan ne a shafin sada zumunta na hukumar, inda ya ce dakarun hukumar ‘yan sandan sun ceto masu aikin yi wa kasa hidima da aka sace a ranar 9 ga Maris a hanyar Funtua zuwa Gusau.

Masu yi wa kasa hidimar da aka ceto sun hada da Oladehin Paul, Ojo Temitope da Ojewale Elizabeth da Adenigbuyan Adegboyega, kuma yanzu haka an mika su da dirkatan hukumar NYSC na jihar Zamfara yayin da shi kuma Mohammed Ardo, wanda aka ceto tare da su an mikashi ga iyalan sa.

Idan dai ba a manta ba, an yi garkuwa da wasu masu aikin yi wa kasa hidima a lokacin da su ke kan hanyar su ta zuwa jihar Zamfara domin gabatar da ayyukan da aka daura musu, matakin da ya sa aka baza jami’an tsoro wanda daga karshe su ka ceto su daga hannun wandan su su ka sace su.

Leave a Reply