Home Labaru Garkuwa Da Mutane: Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sace Wani Soja A...

Garkuwa Da Mutane: Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sace Wani Soja A Zaria

645
0

Masu garkuwa da mutane sun sace wani soja mai mukamin Lieutenant mai suna A. Falana a lokacin da ya je wani shago domin yin cefane a garin Zaria da ke jihar Kaduna.

Mutanen da suka shaida faruwar lamarin sun sahidawa manema labarai cewa, sojan bai sa kaki ba, sannan ya je shagon ne domin siyan kayan abinci, sai batagarin su ka yi awan gaba da shi.

Rahotanni sun tabbarar da cewa, an sace sojan ne a yammacin ranar Litinin din da ta gabata, amma wata majiya daga rundunar ‘yan sanda ta ce tuni sojan ya kubce daga masu garkuwa da dashi ba tare da wani abu ya faru da shi ba.

Sai dai rundunar sojin ta musa faruwar lamarin tare da jaddada cewa, hakan bai faru ba.