Home Labaru Garkuwa Da Mutane: An Sace Dan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna

Garkuwa Da Mutane: An Sace Dan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna

284
0
An Sace Dan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna
An Sace Dan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da dan masalisar dokokin jihar Kaduna Suleiman a babban hanyar Kaduna zuwa Zaria. 

Kranta wannan: Kisan Rabaren: IGP Ya Yi Umurnin Tsaurara Matakan Tsaro A Cibiyoyin Bauta

‘Yan ta’addan sun yi awon gaba ne da dan majalisar dokokin mai wakiltar Zaria a lokacin da yake tuka motarsa kusa da garin Farakwai a ranar Juma’ar nan.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Yakubu Sabo, a lokacin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an gano katin shaida da kuma motar dan majalisar a wajen da abin ya faru.

Ya ce rundunar ta baza jami’anta da suka hada da na cibiyar yaki da ayyukan ta’addanci, da ta yaki da fashi da makami a yankin da abin ya faru domin fafutukar ganin an kubutar da dan majalisar.