Garkuwa Da Mutane: An Nemi Fansar Naira Miliyan 1 A Kan Ma’aikatan FRSC 2
Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa reshen jihar Osun, ta ce wadanda su ka yi garkuwa da ma’aikatan ta biyu sun nemi a biya su Naira Miliyan daya kafin su sake su.
Ma’aikatan da lamarin ya shafa kuwa sun hada da wani Bayegunmi da kuma Abioye, wadanda aka sace a hanyar Iwaraja da ke karamar hukumar Oriade a ranar Litinin da ta gabata.
Kakakin hukumar Bisi Kazeem da na rundunar ‘yan sanda na jihar Osun Folashade Odoro su ka tabbatar wa manema labarai haka.
A cikin wata sanarwa da ya raba wa manema Labarai, Kazeem ya ce mai dakin daya daga cikin ma’aikatan da aka yi garkuwa da su, ta ce maharan sun kira ta sun bukaci a aika masu Naira miliyan daya kafin su sake shi.