Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Garkuwa Da Mutane: Amurka Ta Gargadi Amurkawa Akan Zuwa Najeriya

Kasar Amurka ta gargadi ‘yan kasar ta su yi takatsantsan da zuwa Najeriya saboda yawaitar miyagun laifuka da suka hada fashi da makami, satar motar, ta’addanci, garkuwa da mutane, fyade, su ka zama ruwan dare.

A cikin wata sanarwa da Amurka ta fitar a shafin ta na yanar gizo ta sa Najeriya cikin jerin kasashe masu alamar ‘K’ ga matafiyya, ma’anna mutane da ke fuskantar barazanar a sace su ko ayi garkuwa da su.

Sabuwar  kalmaa ‘K’ na daya daga cikin bayanai da Amurka ta ba ‘yan kasar ta masu tafiye-tafiye, saboda su dauki matakin da ya dace kafin su tafi kasashen duniya.

Sauran kasashen da aka sakawa alamar gargadi na ‘K’ da ke nuna yawaitar satar mutane ko garkuwa da su sun hada da: Afghanistan, Algeria, Angola, Bangladesh, Burkina Faso, Kamaru, Central African Republic, Colombia, Democratic Republic of the Congo, Ethiopia, Haiti, Iran, Iraq, Kenya.

Sai kuma Lebanon, Libya, Malaysia, Mali, Mexico, Niger, Najeriya, Pakistan, Papua New Guinea, Philippines, Rasha, Somalia, South Sudan, Sudan, Syria, Trinidad and Tobago, Turkey, Uganda, Ukraine,Venezuela, da Yemen.” A cikin Najeriya, kasar ta Amurka ta ce jihohin Borno, Yobe da Adamawa ne suka fi hatsari.

Exit mobile version