Gwamnatin Tarayya ta ce aƙalla almajirai miliyan 30 da yara marasa zuwa makaranta miliyan 20 ne suke gararamba a tituna a faɗin Najeriya.
Shugaban hukumar kula da ilimin Almajirai da yara marasa zuwa makaranta ta Ƙasa (NCAOOSCE), Dokta Muhammad Idris, ne ya sanar da haka tare da jaddada buƙatar kulawa da su da kuma sama wa rayuwar su alkibla ta gari.
A jawabin sa yayin ƙaddamar da kwamiti da aka kafa domin sake fasalin ilimin almajirai na tsangaya, Muhammad Idris ya ce,
Baya ga koyon munanan dabi’u, mutane da dama suna cin moriyar raunin yara almajirai.
Muhammad Idris ya kuma ɗora wa kwamitin alhakin haɗa kungiyoyin makarantun tsangaya da ke faɗin Najeriya a ƙarƙashin inuwa guda ta yadda za a iya zaƙulo da malamai masu nagarta daga cikin su,
Da kuma yaukaka hulɗa da haɗin kai da hukumar NCAOOSCE.
Da yake tsokaci, shugaban kwamitin, Sheik Sayyadi Alqasim, ya tabbatar da cewa za su yi aiki tuƙuru domin ganin sun kammala aikin su yadda ya kamata a cikin lokaci cikin inganci.