Home Labaru Garambawul: Gwamna Fintiri Ya Sallami Ma’aikatan Kananan Hukumomi

Garambawul: Gwamna Fintiri Ya Sallami Ma’aikatan Kananan Hukumomi

371
0

Rahotanni na cewa, gwamna Ahmadu Fintiri na Jihar Adamawa ya bada umarnin korar dukkan ma’aikatan kananan hukumomin da a ka dauka aiki daga watan Afrilu na shekara ta 2016 a jihar.

Fintiri ya ce ya dauki matakin ne domin an dauki ma’aikatan aiki ne ta bayan fage.

Gwamnan dai ya bada umurnin ne a lokacin da ya yi wani zama da ma’aikatar kula da kananan hukumomi da masarautu da Daraktocin ma’aikatar kudi ta jihar Adamawa.

Ahmadu Fintiri ya bada sanarwar cewa, za a dawo da shirin ciyar da daliban makarantun kwana na gwamnati da ke kananan hukumomi 21 a fadin jihar.

Leave a Reply