Kasashen Amurka da Nijeriya da tsibrin Jersey, sun ce za su raba sama da dala 267 da tsibrin Jersey ya kwato daga cikin irin kudaden da ake tunanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha ta boye a wasu bankunan kasar.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne, gwamnatin kasar tsibrin Jersey ta sanya dalar Amurka 267 a wani asusun musamman da ta ware domin irin wadannan kudade da su ke kama da na ganima.
Wani ma’aikaci a ofishin ministan shari’a na kasar ya shaida wa manema labarai BBC cewa, har ya yanzu kasar Jersey ba ta gama tantance hanyoyin da za ta bi domin kasafta kudin ba, amma ta ce za ta zauna da kasashen Amurka da Nijeriya domin lalubo hanyar da za su raba kudin a tsakanin su.
Da jimawa wata babbar kotu ta kasar Amurka ta binciko wadannan kudaden wanda ta bayyana cewa sun fito daga Najeriya daga wasu bankuna na kasar Amurka, daga baya kuma aka tura kudin zuwa bankunan tsibirin Jersey.