
Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, ya ce babban kuskure ne Bola Tinubu ya tafka, lokacin da ya yi wa Shugaba Buhari barazanar cewa yanzu lokacin sa ne don haka a ba shi mulki a huta.
Bola Tinubu dai ya yi barazanar ne, lokacin da ya ke jawabi kafin zaɓen fidda gwani a Gidan Gwamnatin Jihar Ogun.
Yayin da ke barzanar dai, Tinubu ya yi wa Buhari gorin yadda ya taimake shi ya zama shugaban ƙasa, kuma kafin shi ya ce ya goyi bayan Atiku Abubakar da Nuhu Ribadu a baya.
Sai dai a cikin wata wasiƙa da Obasanjo ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce furucin lokaci na ne yanzu a ba ni a huta da Tinubu ya yi babban kuskure ne ga shugabancin Nijeriya a yanzu.
Obasanjo, ya ce ba za a iya bunƙasa ƙasa ta zama ƙasaitacciya a ƙarƙashin wanda ya yi irin wannan barazanar ba, balle har a samu nagartar zamantakewa tsakanin ‘yan Nijeriya.













































